Take a fresh look at your lifestyle.

APC Arewa Maso Yamma Sun Amince Da Shugabancin Tinubu

62

Jam’iyyar APC shiyyar Arewa maso Yamma ta kada kuri’ar amincewa da shugaban kasa Bola Tinubu kan yadda ya kawo sauyi.

Da yake tashi daga taron masu ruwa da tsaki na shiyyar da ya gudana a Jihar Kaduna kakakin majalisar wakilai Honarabul Tajudden Abbas ya gabatar da kudirin wanda gwamnan Jihar Kebbi Mohammed Nasir Idris ya amince da shi.

Kudurin wanda masu ruwa da tsakin jam’iyyar da suka halarci taron suka tabbatar sun hada da; Shugaban jam’iyyar APC na kasa Abdullahi Ganduje da mataimakin shugaban majalisar dattawa Sanata Barau Jibrin da ministan kasafin kudi da tsare-tsare na kasa Atiku Abubakar Bagudu da gwamnan Jihar Jigawa Umar Namadi sai mai masaukin baki Uba Sani Gwamnan Jihar Kaduna da tsohon gwamnan Jihar Katsina Aminu Masari da dai sauransu.

Yayin da yake mikawa shugaban kasar kuri’ar amincewa shugaban majalisar ya ce gwamnati mai ci ta yi wa shiyyar aiki da kyau ta fuskar nade-nade da kuma goyon bayan ci gaban ababen more rayuwa.

A cewar Abbasn “A madadin shiyyar Arewa maso Yamma ta APC ina mai jaddada kudirin neman amincewa da shugaban mu kuma babban kwamandan rundunonin soji na Tarayyar Najeriya Sanata Bola Tinubu bisa manufarsa na gudanar da mulki jagoranci mai cike da rudani da goyon baya da kuma bayar da gudunmawa ga ci gaban zamantakewa da tattalin arziki na shiyyar Arewa maso Yamma.”

Shugaban majalisar ya kuma bayyana cewa shugaba Tinubu ya kasance Dan takarar shugaban kasa na shiyyar a zaben 2027 mai zuwa.

Har ila yau gwamnan Jihar Kebbi ya yaba da salon jagorancin gwamnatin shugaba Tinubu wanda ya ce ya sanya kasar nan a matsayin da ta dace a cikin kwamitin kasashe.

Sauran masu ruwa da tsaki a taron sun kuma lura da manyan ayyukan samar da ababen more rayuwa da ake kammala ko kuma ake gudanarwa a yankin Arewa maso Yamma wanda ke nuna sabon zamani na ci gaba a yankin.

Taron ya yi nuni da cewa jam’iyyar APC na ci gaba da bunkasa cikin da hadin kai da kuma kira ga kasa baki daya saboda godiyar da ‘yan Najeriya ke yi wa shugaban kasa da gwamnonin APC.

Aisha.Yahaya, Lagos

Comments are closed.